Mutane hudu ne suka mutu, wasu 9 kuma suka jikkata sakamakon wata ambaliyar ruwa da ta afku a kudu maso yammacin kasar Sin a ranar Asabar din nan, kamar yadda hukumomin yankin suka bayyana.
Hotunan da kafafen yada labaran kasar Sin suka wallafa sun nuna yadda ruwa ke gudu cikin sauri a wani kogi da ke wajen birnin Pengzhou na lardin Sichuan.
Ana iya ganin ’yan yawon bude ido da suka fara wasa a cikin ruwan da ba shi da zurfi, suna ta guduwa domin tsira da rayukansu, suna kuma yin taho-mu-gama da duwatsu yayin da ruwan ya yi awon gaba da su, amma wasu sun kasa isa bakin kogin cikin kankanin lokaci.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Akalla mutum daya, wata mata da ke makale a kan wani dutse a tsakiyar kogin, da alama ta rasa kafar dafawa, kuma abin da ke faruwa a halin yanzu ruwan ya tafi da ita, kamar yadda wani faifan bidiyo da jaridar Daily Youth mallakar gwamnatin kasar ta wallafa ta yanar gizo ta nuna.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/mayakan-taliban-sun-lakadawa-mata-masu-zanga-zanga-duka-a-afghanistan/
A wata sanarwa da hukumomin bayar da agajin gaggawa na Pengzhou suka fitar ta ce, “Ya zuwa karfe 7.30 na dare, ambaliyar tsaunin ta kashe mutane hudu, uku kuma suka sami kananan rauni, sannan wasu shida suka jikkata.”
Ambaliyar ruwan ta zo ne a lokacin bazara da ake fama da matsanancin yanayi a kasar Sin, inda birane da dama ciki har da Shanghai suka bayyana kwanakinsu mafi zafi da aka taba samu a lokacin tsananin zafi a watan Yuli.
Masana kimiyya sun ce matsanancin yanayi a duniya ya zama ruwan dare saboda sauyin yanayi, kuma da alama zai yi tsanani yayin da yanayin zafi ya karu.
Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya bayar da rahoton a ranar Asabar din nan cewa, hukumar sa ido ta kasar Sin ta ba da sanarwar gargadi game da yanayin zafi mai tsanani, yayin da ake sa ran za ta haura ma’aunin Celsius 40 (Fahrenheit 104) a sassan kasar a karshen mako.
Ambaliyar ruwa mai tsanani a kudancin China a watan Yuni ya raba mutane fiye da rabin miliyan da muhallansu tare da haddasa asarar tattalin arziki da aka kiyasta da dala miliyan 250.
CHANNELS TV