Mai Unguwar Jiƙata dake ƙarƙashin karamar hukumar Mani a jihar Katsina ya rasa yara huɗu sakamakon ambaliya ruwan sama da ta ritsa da su a yankin.
Wani mazaunin yankin ya shaidawa jaridar Vanguard cewa lamarin ya ritsa da yaran ne a lokacin da suke ƙoƙarin tsallaka wata gada a yayin da ambaliyar ruwan ta tafi dasu.
“A lokacin da suka fara hawan gadar ruwan bai yi ƙarfi ba, amma da suka yi nisa sai ruwan ya tafi dasu kuma ya zama ajalinsu”.
https://dimokuradiyya.com.ng/ambaliyar-ruwa-ya-sake-mamaye-kauyuka-a-kananan-hukumomin-adamawa/
Biyu daga cikin yaran an samo gawarsu a ƙauyen Hamcheta, sauran biyun kuma aka samu gawarsu a ƙauyen Magami.
Babur din nasu kuma an samo shi daidai gadar da ruwan ya tafi da su.
Tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Aliyu Sabiu Muduru, ya jajantawa Mai Unguwar sakamakon rashin da yayi tare da fatan Allah ya jikan yaran.