Akalla mutane hudu ne suka mutu sannan wasu suka jikkata sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a kauyukan Nyelleng da Gwabi na karamar hukumar Pankshin ta jihar Filato.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Daga cikin wadanda suka mutu akwai wasu ma’aurata da aka bayyana sunayensu da Daniel Goma da matarsa da kuma wasu mutane biyu. Shugaban karamar hukumar Audu Kak’mena ya ziyarci al’ummar yankin domin jajantawa al’ummar yankin.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa ruwan sama kamar da bakin kwarya ya afku a yankin ne tsakanin ranar Litinin 22 da Laraba 24 ga watan Agusta inda ya mamaye yankin kuma gada daya tilo da ta hada yankin da sauran al’ummomi ta nutse. Gadar da aka ce a ko da yaushe tana fama da matsalar a duk lokacin damina kuma al’umma na bukatar a magance matsalar.
Karanta kuma: Za A Fuskanci Mummunan Ambaliyar Ruwa A Abuja
Wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su mazauna yankin ne da ke dawowa daga wata kasuwa da ke makwabtaka da su, kuma suna kokarin ratsawa cikin ruwan amma suka rasa rayukansu a cikin lamarin.
Shugaban Majalisar ya shaida wa jama’ar cewa Majalisar za ta bayar da wasu taimako sannan kuma ta ba da shawarar irin wannan ga Jiha da Hukumar ba da agajin Gaggawa ta Kasa don shiga tsakani sannan ya shawarci mazauna yankin da su yi taka-tsan-tsan wajen tsallaka koguna a lokacin damina domin guje wa sake afkuwar wannan mummunan lamari.
Audu ya ziyarci gidan ma’auratan da kuma na Nendirmwa Kamshinen, wata mata mai juna biyu da ta samu raunuka sakamakon ambaliyar ruwa.
A wani labarin kuma: Buhari Ya Ja Hankalin Duniya Kan Ambaliyar Ruwan Pakistan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ja hankalin duniya game da ambaliyar ruwan data afku a kasar Pakistan.
Shugaban kasar, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar, ya jajantawa yadda ambaliyar ruwan teku ta bayyana a matsayin bala’i mafi muni a tarihin kasar.