Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi da sanyin safiya ya yi barna a yankin Nasarawo Demsa da ke karamar hukumar Demsa a jihar Adamawa.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Wasu majiyoyi sun ce ruwan sama da aka fara da karfe 2 na daren Lahadin nan, ya dauki tsawon sa’o’i da dama, lamarin da ya kai ga ambaliya ta shiga gidaje, shaguna, makarantu, da wuraren ibada tare da lalata wasu kayayyaki masu daraja.
Mazauna yankin da suka nuna damu kan ambaliyar sun ce ya zama mai gama duniya ruwan dare, inda suka dora laifin kan rashin magudanar ruwa.
Wani mazaunin al’ummar da abin ya shafa, Hali Yohana wanda ya ce shi da kansa abin ya shafa, ya ce yankin na fuskantar bala’o’in ambaliyar ruwa a duk lokacin saukar rahamar Ubangiji a cikin al’ummar.
Karanta kuma: Mummunan Ambaliyar Ruwa Ta Hallaka Mutum 10
Ya ce, “Duk lokacin da aka yi ruwan sama, sai ya bazu zuwa gidajenmu da shaguna, yana lalata mana kayanmu, kuma a lokuta da dama, yanaa rushe gidajenmu da shinge.”
Yayin da Hali ya bukaci gwamnati da ta shiga cikin lamarin, wani mazaunin garin Jabir Gambo, ya zargi hukumomi da rashin damuwa, ya kuma yi kira ga ‘yan uwansa da su manta da gwamnati, su yi aiki da kan su domin ceto dukiyoyinsu.
DAILY POST ta ruwaito cewa Demsa, inda aka samu ambaliyar ruwa da safiyar Lahadin, da ke karamar hukumar Suburban bayan gari ce da ke kan iyaka da karamar hukumar Yola ta Kudu, wacce ke da Yola ta Arewa da Girei kusan babban birnin Yola ne.
An sami irin wannan ambaliya a makon da ya gabata a Girei.
A wani labarin daban kuma: Atiku Ya Dira A Kano Don Karbar Mambobin NNPP Da Suka Sauya Sheka Zuwa PDP
A ranar Lahadi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya isa Kano tare da wasu manyan jami’an jam’iyyar.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, Atiku zai karbi bakuncin Sanatan Kano ta tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da magoya bayansa da ake sa ran za su sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa PDP, ranar Litinin mai zuwa.