Ambaliyar ruwa ta mamaye kauyuka masu yawan gaske a kananan hukumomi Bakwai daga cikin 21 na jihar Adamawa.
Ibtila’in ambaliyar ya biyo bayan saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka tafka a makon da ya gabata.
Dubban mutane ne suka rasa muhallansu a sanadiyyar ambaliyar, jami’an agaji sun bayyana ambaliyar ruwan a matsayin mafi muni da aka taba fuskanta a jihar Adamawa.