Adadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ta yi barna a yankin gabar tekun da ke kusa da birnin Durban mai tashar jiragen ruwa na Afirka ta Kudu ya kai fiye da mutum 250, kamar yadda jami’an kasar i suka bayyana.
Tun da farko an kiyasta cewa akalla mutane 59 ne suka mutu a lardin KwaZulu-Natal.
Nomagugu Simalane, ministan lafiya na KwaZulu-Natal, ya shaidawa kafar yada labarai ta eNCA ta Afirka ta Kudu cewa mutane 253 ne suka mutu a halin yanzu, yayin da adadin ke ci gaba da karuwa.
Sai dai Kuma, Kamfanin dillancin labaran reuters ya ce yanzu haka jami’an larduna sun ce adadin ya kai 259.