Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jahar Sokoto yace zai hada hannu da babbar kungiyar nan ta duniya mai tallafawa lafiya da karatun kananan yara watau UNICEF domin shawo kan cututtuka da aka gano. Kamar yadda Jaridar Tvcnews ta wallafa a shafinta
Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana hakane lokacin da ya karbi bakuncin wakilin kungiyar ta UNICEF daga Kano wanda Mista Maulid Wafa ke jagoranta a gidan gwamnatin Sokoto.
Yace gwamnatin za ta kara himma wajan shawo kan matsalar Mata masu ciki da kuma yawan mutuwar kananan Yara da sauran cututtuka dake addabar Jahar.
KARANTA:- WASANNI: Marcus Rashford zai yi jinyar wata uku sakamakon tiyata da za’ayi masa a kafada
Yace gwamnatin sa a shirye take tsaf don hada guiwa da duk wata Kungiya domin cimma kudirorin sa na daukaka Jahar Sokoto.
A cikin wani bayani da mataimakin gwamnan na kafafen sada zumunta Muhammad Bello cewa yayi gwamna Aminu Waziri Tambuwal yayi amfani da tallafin da yake samu wajan kananan asibitoci wajan gyara sama da 230 da kuma nufin gina wasu Asibitocin a nan gaba tare da wadata Asibitocin da Magunguna.
Gwamnan yace a halin yanzu jahar tana da kananan asibitoci kimanin 600.
Ta fannin tsaftataccen ruwan sha, gwamnan yace ya samu babbar cigaba bayan hadin guiwa da yayi tsakanin sa da kungiyar UNICEF, hadi da kashin da mutane keyi a waje.
Yayi bayani a kan tsarin tsaftace Najeriya inda Aminu Waziri Tambuwal din yace Ina bada goyon bayan haka, yace karkashin haka gwamna ya samar da kwamitin da ke kula da cigaban kauyuka da burane, sannan ta nan fannin ma zaiyi kokarin hada kai da ita kungiyar ta UNICEF.
A lokacin jawabinsa shi mista Wafa cewa yayi, Ina matukar farin ciki da jindadin kan yadda muke cin moriyar hadin kanmu da Jahar Sokoto.
Yace shiga cikin rayuwar Al’umma wani abune wanda ya kamata a maida hankali akansa, ya kuma Kira Sarakunan gargajiya da su bada gudun mawansu a wannan fannin.
A cikin bayanin ta shugaban WASH UNICEF NIGERIA tace za mu bayar da tallafin miliyan goma na galan din ruwa don cigaban tsafta, wanda hakan ba zai yiwu ba ba tare da sauya dabi’un mutane ba.
Comments 1