Kungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da harin da aka kaiwa ‘yan kasuwa a Kasuwar Ibdan wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka.
Kakakin kungiyar Isa Sanusi ya shaidawa kamfanin yada labaran AFP cewar an kai harin kan Yan kasuwar ne ranar juma’ar da ta gabata, a kasuwar Sasa kuma an samu rasa rayuka, duk da yake basu iya tantance yawan mutanen da suka mutu ba.
Kamfanin AFP yace a cikin makwannin da suka gabata, ana fama da kalamun batunci da ake yiwa Yan arewacin kasar da kuma kai hare hare kan matsugunan Fulani makiyaya da ake zargi da aikata laifuffuka a Yankin Jihohin Yarbawa.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yayi Allah wadai da tashin hankalin, inda ya bukaci hukunta masu aikata laifuffuka ba tare da shafawa wata kabila karar tsana ba.