Hukumar kare hakkin ɗan Adam ta duniya Amnesty International, tayi alawadai da kama Nastura Sharif, sakamakon jagorantar zanga-zangar lumana ga gwamnatin Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Mai magana da yawun hukumar Isa Sanusi ne ya bayyana haka ta hanyar aikewa da jaridar Punch da sakon kar ta kwana, inda yace lallai ne gwamnatin tarayyar Najeriya da tayi saurin sakinsa.
Sanusi ya rubuta “dole ne hukumomin Najeriya su saki Nastura Ashir Sharif, saboda bai aikata komai ba face gaskiya da kuma kare rayukan al’umma”.
Yace ba abinda ya aikata face kiran gwamnati da tayi abinda ya dace, hakan na nuni da cewa Gwamnatin Buhari ta hana fadar ‘yancin baki da kuma ‘yan magana kamar yadda yake kundin tsarin mulkin ƙasar nan.
Daya daga cikin ‘ya’yan kungiyar Coalition of Northern Groups, mai suna Aminu Adamu ya bayyana cewa shugaban hukumar ‘yan sandan jihar Sanusi Buba ne ya aike musu da sakon gayyata, da isarsu aka kama wanda ya jagoranci zanga-zangar.
Da aka tuntubi kakakin hukumar ‘yan sanda na babban birnin tarayya Frank Mba, domin jin ta bakinsa ya bayyana cewa bai ma san an kama wani mai suna haka ba.
Idan ba a manta ba fadar gwamnatin tarayya ta gargadi matasan da su daina zanga-zangar saboda zata iya shafar aikin jami’an tsaro a jihar ta Katsina.