Kungiyar Fulani ta, Miyetti Allah Kaute Hore, ta nemi gwamnatin tarayya da ta kama shugabannin nahiyar kudu maso yammacin kasar nan ta kuma tuhume su da kafa kungiyar tsaro a yankin na su mai suna Amotekun.
Cikin wata zantawa da ya yi da manema labarai, shugaban kungiyar na kasa, Bello Bodejo, cewa ya yi an kafa Amotekun din ne da nufin ganin an karar da al’ummar Fulani daga doron kasa.
A ranar Laraba, kungiyar ta nemi Gwamnonin shiyyar da su jingine batun kafa kungiyar ta Amotekun, a sakamakon bayanan da babban Lauyan gwamnatin tarayya Ministan shari’a Abubakar Malami ya yi, inda ya bayyana cewa, haramun ne kafa wannan kungiyar.