By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an tsaron jihar Ekiti mai suna Amotekun sun damke wasu maza biyu da kananan yara biyu bisa laifin yin sata a wasu al’ummomin jihar.
Mutanen biyu daya daga cikin su wanda ya kasance ma’aikacin wutar lantarki, mai shekaru 35, Taiye Ajakaye; da kuma mai gadin dare Gbenga mai shekaru 45, an kama su ne ranar Litinin a Ilawe Ekiti bisa laifin shiga wani shago da dare tare da sace buhunan koko guda biyu.
Ajakaye, wanda ya amsa laifinsa, ya ce, “Buri na shi ne in sayar da kokon domin in samu kudi don in ji dadin rayuwata.
“Na aikata wannan aika-aika ne tare da mai gadi da shirin cewa mai kantin zai yi zargin cewa wasu matasa da suka yi fashin kantin ne tun da farko.
“Na shirya sayar da kokon kan kudi naira 200,000. Shi ya sa na kai jakunkunan zuwa Ado Ekiti, amma na mayar da su gida a lokacin da na kasa samun mai sayen kayan amfanin gona a ranar Lahadin nan data gabata.
“Watakila ana shirin kai kayan amfanin gona zuwa Ado Ekiti ne wasu suka gani suka sanar da Amotekun wanda hakan yasa suka zo su kama ni.”
Amma mai gadin dare, wanda ya ce ya shafe shekaru sama da 20 yana tsaron yankin, ya musanta cewa yana da hannu a cikin lamarin, yana mai cewa, “Ya yi karya ya tsara ni, Ban san komai game da shi ba. Lokacin da na gano an yi wa kantin sayar da barasa sata a wannan dare, sai na yi namijin kokari da mai shagon kan yadda za a nemo wadanda suka aikata laifin.”
A wani labarin kuma, an kama wasu kananan yara biyu da wadanda suka kammala makaranta mai suna Aina mai shekaru 16 da Ibrahim mai shekaru 17 a Iyin Ekiti ranar Talata bayan yunkurin yin sata a gidan wata sakatariyar dindindin ta al’umma mai ritaya.
Aina ta ce shi da Ibrahim sun je gidan da gangan don su kwashi duk abin da za su iya dauka.
Yarinyar ta ce, “Lokacin da muka isa wurin, Ibrahim ya ce in shiga, amma abin takaici ni, matar PS mai ritaya ta ganni, sai na tsere cikin silin na boye. Amma sun gano ni sun kuma kama ni. A lokacin, ba a iya samun Ibrahim ba, sai da aka kama shi a garin”.
Kwamandan Rundunar Amotekun, Brig. Janar Joe Komolafe (mai ritaya), ya ce, “Mutanenmu sun kama su ne bayan tattara bayanan sirri. Muna ba da bayanin su. Za a mika su ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincike da gurfanar da su a gaban kotu.”