Akalla Fulani 37 da dabbobi 5,000 ne kungiyar tsaro ta Amotekun ta cafke a jihar Ondo saboda karya dokar gwamnatin jihar na umurnin da ta ba Fulanin na ficewa daga dazuzzukan jihar.
An cafke su ne a wani dajin gwamnati da ke Ala, Oda da kuma Ofosu.
Idan za a iya tunawa Gwamna Rotii Akeredolu ya bai wa Fulanin wa’adin kwanaki 7 dasu fice daga cikin dazuzzukan gwamnatin jihar.
Da wannan, Akeredolu ya umurci makiyayan da su yi rejista da gwamnati domin ba su damar yin kiwo a cikin dazuzzukan ba tare da an kore su ba.
Shugaban kungiyar Amotekun a jihar, Chief Adetunji Adeleye ya tabbatar da cafke makiyayan wadanda suka gaza cika ka’idojin da gwamnatin jihar ta sanya.
Adeleye ya kara da cewa sauran makiyayan sun cika wadannan sharudda, kuma sun yanke shawarar ficewa daga dazuzzukan jihar.
Ya ce tabbatar da bin wannan doka ta gwamnati na ci gaba da gudana, sakamakon jami’an kungiyar da ke bi daji daji suna zakulo Fulanin da suka bijirewa wannan doka.
A cewarsa: “Wasu daga cikin su sun amince da barin dazuzzukan jihar sakamakon gaza cika wadannan sharudda.
“Sun biyo hannun shugaban kungiyar Miyatti Allah na jihar. Wasu sun yanke shawarar komawa Osun, Edo da kuma jihar Kogi.
“A yanzu jami’anmu na kan iyakokin wadannan jihohi. Ya zama wajibi mu sa ido kan hijirarsu domin tabbatar da cewa ba su lalata gonaki akan hanyarsu ba.
“Za mu gabatar da wadanda muka kama ga shugaban su domin tasar keyarsu, idan kuwa suka ki, to gwamnatin jihar za ta dauki mataki.”
Adeleye ya yi kira ga manoman jihar da su rinka kiran jami’an Amotekun da zaran sun ga shanu sun shiga cikin gonakinsu domin kare gonakinsu daga lalacewa.