Gwamnatin Amurka ta ce ba ta goyon bayan wani mutum ko dan takara ko jam’iyya gabanin babban zaben Najeriya.
Molly Phee, Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka kan Harkokin Afirka ce ta bayyana hakan a ranar Laraba, a Abuja.
KU KARANTA: Sam Emefele Bai Cancanci Zama Gwamnan CBN Ba – Inji Wani Gwamna
“A nan Najeriya, ra’ayi na ne cewa abubuwan da suka kamata a nan suna da karfi sosai kuma Shugaba Buhari ya bayyana karara cewa ba zai sake neman wa’adi na uku ba, kuma yana da burin mika mulki lami lafiya.
“A watan Disamba, lokacin da kasar Amurka ta karbi bakuncin taron shugabannin kasashen Afrika, shugaba Biden ya gayyaci wasu zababbun shugabannin Nahiyar zuwa fadar White House ciki har da shugaba Buhari domin tattaunawa kan zabe mai zuwa a 2023.
“A wannan taron, sun tattauna mahimmanci da kalubalen yadda za a shirya zabe na gaskiya da adalci wanda zai haifar da sahihin sakamako, da kuma yadda za a tabbatar da an gudanar da zaben cikin lumana.
“A bara, gwamnatin ku ta aiwatar da daftarin gyare-gyaren zabukan da ke da inganci kuma sun ba da gudummawa, na yi imani da ingantaccen tsarin zaben.
“Kamar yadda muka yi zabe mai nasara a Amurka, wanda hakan ke bukatar kowa ya bayar da gudunmawarsa, shi ya sa kamar yadda na fada a baya, yana da kyau dukkan ‘yan Najeriya su yi aiki da gaskiya, kuma su zabi wanda suke so.
“A fahimtata cewa ‘yan Najeriya sun amince da wannan tsarin zabe kuma ya kamata su kada kuri’a da kwarin gwiwa cewa kuri’unsu za ta yi amfani” in ji Phee.
A wani labarin kuma, An Cafke Shugaban EFCC A Abuja Amma Na Bogi
Hukumar dake Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa zagon kasa EFCC ta kama wani dan damfara, mai suna Salman Umar Hudu, dan kimanin shekaru 38, da ya kasance dan jihar Kano, bisa laifin sojin Gona.
A cewar hukumar, an kama Hudu ne a wani otel da ke Abuja saboda ya bayyana kansa a matsayin shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ga wasu jami’an hukumar, domin dai cimma wata manufa tasa ta kashin kai.