Firaministan Pakistan Imran Khan ya yi yunkurin nuna Amirka a matsayin kasar da ba ta da dattaku.
A yayin jawabinsa ga Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya a ranar Juma’ar da ta gabata, Khan ya ce Pakistan ta dandana rashin godiya da rashin tsayayyar maganar da Amurka ke nuna wa kasashen duniya.
Firaministan ya ce wasu ‘yan siyasar Amurka da Turai na zargin Pakistan da hannu a Afghanistan. Sai dai ya ce tun daga harin da aka kai wa Amurka na ranar 9 ga watan Satumba, Pakistan ta fara bakin jini saboda kawancen da ta yi da Amurka. Ya ce a karshe ‘yan Pakistan dubu 80 ne suka rasa rayukansu a sakamakon tallafa wa Amurka da kasar ta yi.
”Dalilin wahalar da muka sha shi ne kawancen da muka yi da Amurka a yakin Afghanistan. Ya kamata a ce an gode mana amma sai ga shi ana zargin mu da lalacewar al’amura a Afghanistan.” inji Khan