By Ishaq Dabai
Amurka da Burtaniya sunyi gargadi ga ‘yan kasar su a yau Litinin dasu guji otal-otal a Kabul babban birnin Afghanistan, musamman sanannen otel na Serena.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka tace,’Yan Amurka dake kusa da otal din Serena su fice nan da nan saboda “barazanar tsaro” a yankin.
A cikin sabunta shawarar data bayar na kada ku yi balaguro zuwa Afghanistan, Ofishin Harkokin Waje na Burtaniya yace: “Dangane da karuwar haɗarin dake faruwa, ana baku shawarar kada ku zauna a otal, musamman a Kabul (kamar otal din Serena).”
Serena shine sanannen otal na alfarma a Kabul, wanda ya shahara da masu ziyartar kasashen waje kafin garin ya fada hannun ‘yan Taliban makonni takwas da suka gabata.Sau biyu tana fuskantar hare -haren masu tsattsauran ra’ayi.
Hakan na zuwa ne bayan kungiyar IS ta yi ikirarin mummunan harin bam a birnin Kunduz dake arewacin kasar ranar Juma’a wanda ya ratsa masallaci a lokacin sallar Juma’a harin daya fi zubar da jini tun bayan da sojojin Amurka suka bar kasar a watan Agusta.