Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya ce kasarsa ta Amurka za ta ɗauki tsattsauran mataki kan kaswr Rasha, muddin ba ta shafawa kanta ruwa ba game da kutse ta Intanet.
Wani dan Jarida ya tambayi Mista kan cewa ko akwai hukunci mai tsauri da kasar za ta dauka, nan take ya amsa da cewa Kwarai kuwa.
To sai dai kasar Rasha ta musanta cewa Amurka ta tuntuɓi sau da dama game wannan kutse da ake zarginta da aikatawa.
A ranar juma’a ne Mista Biden da shugban Rasha Vladmir Putin suka shafe tsawon lokaci suna waya bayan wata ganawa da suka yi a birnin Geneva.