Gwamnatin Amurka ta cire ƙarin kuɗin da ta wajabta wa ‘yan Najeriya biya ga masu neman bizar shiga ƙasarta.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Ferdinand Nwonye, ya bayyana a wata sanarwa jiya Juma’a cewa an fara aiki da janye biyan kuɗin daga ranar Alhamis da ta wuce.
Ya ƙara da cewa hakan ya biyo bayan cire wasu tsarabe-tsarabe na neman bizar Najeriya da gwamnatin ƙasar ta sanya wa ‘yan Amurka masu neman shiga Najeriyar.
“Ana shawartar ‘yan Najeriya da ke neman bizar shiga Amurka da su ziyarci shafin www.travel.state.gov domin samun ƙarin bayani,” a cewar Ferdinand Nwonye
Najeriya ta ayyana ƙarin kuɗin neman bizar shiga ƙasar ne a kan Amurkawa bayan ita ma Amurkar ta saka wa ‘yan Najeriya ƙarin kuɗin neman biza.
Daily Trust ta ruwaito cewa ‘yan Najeriyar da suka samu bizar Amurka bayan ƙarin sun biya ƙarin kusan dala 80 zuwa 110 – kwatankwacin naira N28,800 zuwa N39,600.
Yanzu Najeriya ta rage kuɗin neman bizar kan Amurkawa, inda yake kamawa daga dala 180 zuwa 150.
-Rahoton Bbc Hausa