Kasar Amurka ta cire takunkumin da ta Kakaba wa wasu ƙasashe 61 daga shiga kasarta Sakamakon annobar korona.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar lafiyar kasar ta gindaya wasu Ka’idoji da ƙasashen za su bi don kauracewa bazuwar cutar.
Ƙasashe kamar su Faransa da Spaniya da Italiya dukkanin su suna mataki ma uku ne inda ke nufin cewa kowannen fasinja da aka yi masa rigafin cutar ta korona ka iya shiga kasar ta Amurka ba tare da shamaki ba.
Sai dai galibin fasinjoji daga kasar Birtaniya ba za su samu wannam sahalewa ba.
Ko da yake har yanzu akwai wannan takunkumi a kan kasar ta Birtaniya, amma ba wai hakan na nufin cewa takunkumin ya shafi har sa yan Amurka mazauna can bane.
A hannu guda kuma kasar Birtaniyar ta ce wajibi ne duk wanda ya shiga Birtaniyar daga Amurka, to sai an killace shi na tsawon kwanaki goma.