Najeriya da Gwamnatin Amurka sun cimma matsaya kan maido da sama da dala miliyan 23 na dukiyar kasar da ake zargin Abacha ya kai Amurkan.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, An gudanar da taron sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ofishin ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami a ranar Talatar nan.
Yayin da Malami ya sanya hannu a madadin gwamnatin Najeriya, jakadiyar Amurka a Najeriya, Mary Beth Leonard ta sanya hannu a madadin gwamnatin Amurka.
Aranta kuma: Amurka Ta Maido Wa Najeriya Dala Miliyan 311 Na Abacha
A cewar Malami, kudaden da aka dawo da su, za a zuba jari ne a wasu ayyuka guda uku da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa, wadanda suka hada da hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma gadar Neja ta biyu.
A baya dai Najeriya ta kwato wasu kaso daga cikin kudaden da Abacha ya wawure, wadanda ake kyautata zaton gwamnatin mulkin soja ta Janar Sani Abacha ta karkatar da su daga asusun gwamnati a shekarun 1990.
A shekarar 2020, Amurka da Jersey su ma sun amince da mayar da sama da dala miliyan 308 na kudaden da aka karkatar zuwa ga Najeriya.
A shekarar 2006, kimanin dala miliyan 723 da Abacha ya wawushe ya dawo Najeriya daga kasar Switzerland, kamar yadda gidan talabijin na channels ya rawaito.
A wani labarn kuma: Amurka za ta sayar wa Najeriya makamai na dala biliyan daya
Amurka ta amince ta sayar wa Najeriya makamai da kudinsu ya kai na dala biliyan daya da zummar karfafa yaki da kungiyoyi masu rike da makamai.
A wata sanarwa da hukumar hadin kai game da tsaro ta Amurka ta fitar, ta ce Najeriya ta bukaci sayen jiragen helikwafta 12 masu kai hare-hare da makami mai kai hari inda aka nufa ba tare da matsala ba.