Jami’an tsaron Amurka sun ce shugaban yan ta’addan AlQa’eda ya Maraya barzahu, wato dai ya mutu, a kasar Afghanistan yayin wani luguden ruwan alburusai da sukai a karshen mako.
Jagaban yan ta’addan mai suna Ayman Al-zawahiri ya mutu ne yayin ruwan farmaki da jami’an tsaron Amurka suka kaddamar a Afghanistan, kamar yadda suka sanar a ranar Litinin.
Wannan labarin na mutuwarsa na zuwa ne bayan da aka kammala shiryawa don shugaban kasar Amurka Joe Biden ya gabatar da jawabi ga yan kasa kai tsaye, a yammacin yau Litinin.
DUBA WANNAN LABARIN: Duniya na dab da wargajewa – Guttares
Kamfanin dillancin labarai ma Associated Press ya rawaito cewa, tun a karshen mako aka hallaka shi, amma aka jinkirta sanar da hakan har sai da aka tabbatar da mutuwarsa.
Har kawo wannan lokaci fadar mulkin Amurka ta White House bata ce komai ba kan batun kisan dan ta’addan, amma ana saka ran cewa a jawabin da Kome Biden zai gabatar nan gaba, zai tabo wannan batu, dama irin nasarorin da suke samu wajen hada kai tare da yakar ta’adda.
Rahoton ya tabbatar da cewa yayin luguden wutar ba a samu farar hula koda mutum ɗaya, daya jikkata ba.