Mataimakin shugaban kasar Amurka, Kamala Harris, ta bayyana fatan cewa babban zaben Najeriya na shekara mai zuwa zai kasance cikin lumana da kuma nuna ɗa’a ga muradin al’ummar kasar.
Kamala Haris ta yi magana ne a fadar White House bayan wata ganawa da takwaranta na Najeriya, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.
Har ila yau Harris ta yaba da rawar da Najeriya ke takawa wajen tabbatar da dimokuradiyya a yammacin Afirka.
KARANTA ANAN: Sha’aban Sharada Ya Ƙaddamar Da Takararsa A ADP Bayan Shan Kayi A APC
Ta ce: “Nigeria kuma ta kasance muhimmiyar abokiyar tarayya wajen tabbatar da bin ka’idojin kasa da kasa, ko dai magance koma bayan dimokradiyya da muke gani a yammacin Afirka.
Kamala Haris tace shugabannin Afirka, musamman, shugabancin Najeriya, shine mabuɗin tinkarar kalubalen yanki da na duniya.
Ta yaba da tattaunawar da aka yi don karfafa alakar da ke tsakanin Amurka da Najeriya, sannan ta yabawa shirin samar da makamashi na Najeriya (ETP) karkashin jagorancin Osinbajo.
A wani labarin kuma: Gwamnatin Legas Ta Bada Umurnin Komawa Makarantu Ranar Litinin
Gwamnatin jihar Legas ta umarci dukkan makarantu da su fara zagon karatun shekarar 2022/2023 a ranar 5 ga watan Satumbar 2022.
Bayanan hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da babban daraktan ofishin tabbatar da ingancin ilimi na jihar, Abiola Seriki-Ayeni, ya fitar a ranar Asabar.