By Ishaq Dabai
A wani yunƙuri na zurfafa yaƙi da cutar Corona kasar Amurka tana shirin ba da allurar sama da miliyan 17 na allurar J&J COVID-19 daga kayan cikin gida zuwa ga Tarayyar Afirka.
Shugaban kasar Joe Biden shine wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 14 ga watan Oktoba, yayin da yake ganawa da takwaransa na kasar Kenya, Uhuru Kenyatta a Fadar White House.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wannan shine farkon ganawar Biden tare da wani shugaban Afirka.” Sannan yace muna ci gaba da yakar COVID 19″ in ji Biden yayin taron.
Tallafin allurar rigakafin miliyan 50 da Amurka ta riga ta bai wa Tarayyar Afirka tace za’a samar da alluran rigakafin na J&J miliyan 17 nan da nan kuma za a mika su ga Tarayyar Afirka a cikin makonni masu zuwa.
Kenyatta ya gode wa Biden saboda taimakon daya yi wa Kenya da sauran kasashen Afirka, yana mai cewa Amurka ta ‘kara himma’ idan aka zo batun bayar da allurar rigakafi da samun allurar rigakafi ga wasu kasashen.