Annobar Korona ta yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 186 da 462 a duniya tun farkon bullarta a watan Disamban bara a kasar Chana, inda a Amurka kadai, cutar ta kashe kusan mutane dubu 50, da suka hada da dubu 3 da 176 da ta kashe cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Sama da mutane miliyan 2 da dubu 675 suka kamu da kwayar cutar a kasashen duniya 193, yayin da fiye da dubu 700 suka warke kamar yadda Rfi Hausa ta labarto.
Baya ga kasar Amruka da ke sahun gaba wajen samun asarar rayuka, italiya ce ke matsayi na biyu da asarar mutane dubu 25 da 549 , sai kuma dubu 23 da 157 da suka mutu a Spain, yayin da a Fransa, adadin mamatan ya kai dubu 21 da 856, sai kasar Birtaniya da ta yi asarar mutane dubu 18 da 738 a sanadiyar annobar ta coronavirus.