An ɗage Shari’ar Shugaban Ƙungiyar Ƴan Aware ta Inyamurai – IPOB Nnamdi Kanu zuwa 19 da 20 ga watan Janairun Sabuwar Shekara ta 2022.
Wannan na zuwa ne bayan ya bayyana a gaban Mai Shari’a Binta Nyako a Babbar Kotun Tarayya ta Abuja a ranar Laraba.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar, Lauyoyin IPOB sun yi cincirindo a gaban Mai Shari’ar.

KARANTA WANNAN LABARIN: WHO Tayi gargadi kan yiwuwar Fuskantar Karancin Sirinji A 2023
A wani Labarin kuma
Jami’an tsaro a ranar Laraba sun hana Maxwell Opara, ɗaya daga cikin Lauyoyin dake kare tsararren Shugaban Ƙungiyar Ƴan Aware ta Inyamurai — IPOB Nnamdi Kanu, daga shiga Babbar Kotun Tarayya dake Abuja.
Haka zalika, waɗanda aka hana shiga Kotun akwai ƴan jarida, da Shuwagabannin Inyamurai, da masu sanya ido gami da masu kare haƙƙin bil’adama.
Amma sauran Lauyoyin Kanu da suka haɗa da; Ifeanyi Ejiofor, da Aloy Ejimakor an barsu sun shiga a cikin Kotun.
Idan dai ba’a manta ba, Mai Shari’a Binta Nyako ta ɗage shari’ar Kanu zuwa ranar Yau.
Kanu dai na fuskantar ƙararraki, kuma tuni ake tsare dashi a kurkukun Hukumar Jami’an tsaron Ƴan sandan Farin Kaya, tun lokacin da aka sake kama shi a ƙasar waje a watan yunin shekarar 2023.
Ya kuma bayyana cewa bai aikata laifuka guda 7 da ake zargin shi da aikatawa a zuwan shi Kotu na watan Oktoba na shekarar 2021.