Wata Kotu dake zaman ta a Kasuwan Nama dake Jos a ranar Alhamis, ta tura wani matashi ɗan shekara 18 Solomon Paul zuwa gidan yari na tsawon watanni shida, sakamakon satar keken ɗinki da darajar shi takai Naira dubu 70,000.
Jojin Lawal Suleiman ya ɗaure Paul bayan an same shi da aikata laifin guda ɗaya na sata, tare da neman rangwame daga Kotun.
Suleiman ya kuma baiwa wanda aka yankewa hukuncin biyan tara ta Naira dubu 10,000.

KARANTA WANNAN LABARIN: Yadda Yan Majalissar PDP da na APC suka kusan Dambacewa, Bayan Tsige Kakakin Majalissa
Jojin ya kuma umarci wanda ya saci keken ɗinkin daya maida kayayyakin ga wanda ya sace shi.
Tunda farko, mai shigar da ƙarar Ibrahim Gowkat ya shaidawa kotun cewa, ƴan sanda sun kawo ƙara a ofishin ƴan sanda na B a Jos a ranar 29 ga watan Satumba, daga Dachomo Pam.
Mai shigar da ƙarar ya shaidawa kotun cewa a lokacin da ƴan sanda suke bincike, wanda ake ƙarar ya tabbatar da cewa ya saida keken ɗinkin akan kuɗi Naira dubu 1,500 ga wani.
Gowkat yace wanda aka yankewa hukuncin ya kasance yana aikata laifin.
Yace laifin ya saɓawa sashe na 72 na dokar Manyan laifuka ta Filato ta Arewacin Najeriya.