An ɗaure wani mutum kan Lalata Gilashin Gidan Maƙwabcin sa watanni 8
Kotu dake zamanta a Abuja ta ɗaure wani mutum mai suna Dahiru Muhammad mai shekaru 29 a gidan yari na tsawon watanni 8 bisa samunsa da laifin lalata gilashin makwabcinsa da ke Abuja, ranar Alhamis
KARANTA WANNAN LABARIN::Gwamnatin Tarayya Za Ta Kaddamar Da Tallafin Fitar Da ‘Yan Najeriya Miliyan 100 Daga Kangin Talauci
‘Yan sandan sun tuhumi Muhammad da laifin keta haddi, mugun nufi da kuma barna.
Muhammad ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi kuma ya roki a yi masa sassauci.
Alkalin kotun, Sulyman Ola, ya bai wa wanda ake tuhuma zabin biyan tarar N30,000.
Ola ya kuma umurci wanda aka yankewa laifin da ya biya wanda ya shigar da karar naira 195,000 ko kuma ya daure wata uku a gidan yari maimakon diyya.
Ola ya gargaɗi mai laifin da ya daina aikata laifuka.
Tun da farko, Lauyan mai shigar da ƙara, Chinedu Ogada, ya shaida wa kotun cewa, mai shigar da kara, Glory Taiyek, na wannan adireshin ne ya kai karar ‘yan sandan Kubwa a ranar 15 ga watan Yuli.
Ya ce a ranar 12 ga watan Yuli da karfe 6:30 na yamma mai laifin ya je gidan mai ƙarar ya buga mata kofar da dutse amma ta ki bude kofar.
Ya shaida wa kotun cewa daga baya wanda aka yanke wa hukuncin ya dawo da karfe 8:30 na dare tare da tsani, ya samu shiga gidan ya karya gilashin mai karar.
Ogada ya ce a lokacin da ‘yan sanda suke yi wa ‘yan sanda tambayoyi da bincike, wanda ake tuhumar bai iya bayar da gamsasshen bayani kan abinda ake tuhumar sa.