Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da shirin bunkasa tattalin arzikin Fulani karo na hudu, a jihar.
A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a cibiyar koyar da sana’o’i ta Limawa dake nan garin Dutse, shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta jihar Jigawa, Kabiru Umar Dubantu yace gwamna Badaru Abubakar ne ya yi alkawarin shigar da Fulani cikin shirin bunkasa tattalin arzikin alummar jihar.
Yana mai cewa gwamnatin jihar Jigawa tana shigo da Fulani cikin tsare-tsaren cigaban alumma.
Ya kara da cewar an ware kudi naira miliyan arbain da takwas (48) domin sayo shanu dari biyar da kuma awaki da za a rabawa Fulani a matsayin bashi da zasu biya a tsawon shekaru biyu zuwa uku.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar Jigawa tana kan gaba wajen kula da jin dadin Fulani ta hanyar shigo dasu cikin tsare-tsaren gwamnati.
Shugaban na kautal hore ya ce za a cigaba da rabon shanun da kuma awaki a sassan jihar Jigawa a matsayin rance marar kudin ruwa, inda ya bukaci Fulani dasu yi amfani da wannan dama wajen bunkasa tattalin arzikinsu.
A lokacin kaddamarwar, an baiwa Muhammad Abubakar shugaban matasan Fulani da Hajiya Altine Umar, shanu bibbiyu, inda suka godewa kungiyar bisa wannan tagomashi.