Wasu gungun matasa a Katsina a ranar Asabar sun kai hari tare da ƙone wani daga cikin ƴan Fashi da suka ƙwaci mota ƙirar Honda daga hannun wani tsoho mai Shekaru 52 da ake kira Alhaji Usman Abdulmuminu a lokacin da yake duba aiki a gonar sa dake ƙauyen Kirkini na Ƙaramar Hukumar Kankiya ta Jahar.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Katsina SP Gambo Isah ya bayyana haka a lokacin da yake taron Manema Labaru, bayan ya gabatar da gawar Ɗan Fashin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sare Kan Ɗan Majalisa manuniya ce na rashin Doka tsantsa a Najeriya — Shehu Sani
A cewar SP Gambo Isah, ƴan Fashi guda biyar sun zo ne a cikin mota domin ganawa da Manomin a gonar sa. Inda 4 daga cikin su, suka nemi ganawa dashi cikin ruwan sanyi.
Manomi sai ya amince da ganawa dasu a lokacin daya isa, sun fito bindiga inda suka bayyana masa cewa su ƴan Fashi da Makami ne. Sai suka karɓe wayar sa, da kuɗin dake tattare dashi. Sai suka buƙaci ya basu makullan Motar, wanda ya basu.
Manomin yayi saurin sanar da Al’ummar yankin, inda suka yi saurin sanar da DPO na Ƴan Sanda dake yankin. Abun baƙin ciki ga ƴan Fashin shine hanyar da suka ɗauka sai ta kaisu ga matasan da suka bincike su.
A yayinda guda 4 daga cikin ƴan Ta’addan suka tsere, ɗaya daga tuƙa Motar an kama shi, an ji masa dukan tsiya.
SP Gambo Isah a rahoton shi yace ” a ranar 21 ga watan Mayu na shekara 2022, da misalin ƙarfe 12, Rundunar ta samu kiran gaggawa cewa ƴan fashi su biyar sun kai hari ga wani Alhaji Usman Abdulmuminu mai shekaru 52 dake a Ƙaramar Hukumar Charanci tare ƙwace masa mota da darajar ta kai Miliyan 2.6.
“A lokacin bincike an gano bindiga ƙirar Fistin da harsashi. Kuma tuni Rundunar ta fara bincike domin gano sauran da suka tsere
Comments 1