Wani kwamitin hadin gwiwa na Jami’an tsaro ya ƙwato shanu da tumaki guda 500 da aka sace a Ƙananan Hukumomin Shiroro da Kunya na Jahar Niger.
Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da tsaron cikin gida Emmanuel Umar ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga Manema Labaru a Minna a ranar Juma’a.
Yace dabbobin an ƙwato su ne daga ƴan bindiga wanda suka gudo daga wasu Al’ummomin Kuchi, da Galadiman-Kogo, da Alawa, da Erena da Shiroro da Ƙaramar Hukumar Munya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan Sanda a Gombe sun kama mutane 109 akan yunƙurin damfarar mutane, shigowa Najeriya
“Makonni kaɗan da suka wuce, muka gudanar da samame a wasu yankuna, kuma an kulle layukan sadarwa. Mun samu rahoto cewa wasu sun shiga wasu ƙauyuka.
Umar yace akwai waɗanda suka rasa rayukan a cikin jami’an tsaro.
Ya ƙara dacewa ” Gwamnatin Jahar tayi ta’aziyya ga waɗanda suka sadaukar da rayuwar su domin samun zaman lafiya, da waɗanda suka samu raunuka.”
Umar yace dabbobin za’a ajiye su ƙarƙashin kulawar Ma’aikatar kula da Dabbobi.
Kwamishinan yace wannan samame da suke kaiwa zai yi bakin ƙoƙari domin haɗa kai da maƙwabtan jahohi domin cigaba da gudanar dashi.