Wani kwararren likitan yara Dakta Victoria Osamuyi ya shawarci iyaye mata masu ɗauke da juna biyu da su yawaita cin kayan marmari domin amfanar da abunda suke dauke da shi.
Dakta Osamuyi ya bayyana hakan yayin hira da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN yayi da shi a yau, inda yace ta hanyar yawaita cin kayan marmarin zai taimaka yaro wajen samun sinadaran gina jiki da zasu sanya a haifi yaro ɓulɓul.
Ya kara da cewa cin kayan marmarin zai kuma taimakawa mahaifiyar wajen itama ta zama cikin koshin lafiya, baya ga jaririn ta.
”Cin kayan itatuwan zai taimaka wajen kawar da duk wasu laulayi da mata masu juna biyu, kan yi.” in ji Dakta Osamuyi