An ɗage ranar da za a yi wa tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, sutura.
Mai magana da yawun Marigayin Bolaji Tunji ne ya shaida wa manema labarai haka a ranar Juma’a.
“Iyalan marigayin za su sanar da lokacin da za a yi masa jana’iza nan gaba kadan.
“Jana’izar za ta kasance a kebance saboda biyayya ga dokokin Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC)”, inji Mista Tunji.
https://dimokuradiyya.com.ng/da-dumi-dumi-surukin-ganduje-sanata-ajimobi-ya-rasu/
Ya kuma yi kira ga mutanen da ke tururuwa zuwa gidan marigayin domin ta’aziyya da su bi matakan kariya daga kamuwa da COVID-19 kamar yadda hukumar NCDC ta zayyana, ciki har da wanke hannaye, da sanya takunkumin rufe fuska da kuma ba da tazara.
Marigayi Abiola Ajimobi ya rasu ne ranar Alhamis a wani asibiti mai zaman kansa a Legas bayan ya yi fama da wata jinya mai alaka da sarkakiyar da cutar coronavirus ta haddasa.
Yanzu haka dai a faɗin tarayyar Najeriya, ana ci gaba da mika sakon jaje da ta’aziyya ga iyalan mamacin.