Rundunar Yan sandan jihar Bauchi ta sanar da janye dokar hana zirga-zirga da gwamnatin jihar ta sanya a wasu yankuna dake karamar hukumar Bauchi.
Daga cikin wurare da aka sanya dokar sun haɗar da Yelwa, Tsakani, Kagadama, da Kuma Lushi.
Hakan ya biyo bayan lafawar lamura a yankunan, sakamakon yadda aka samu rikici tsakanin wasu mazauna yankunan wanda ya kai ga sanya dokar hana zirga-zirga tsawon awanni 24.
Mai magana da yawun rundunar Ahmed Wakili ne ya sanar da hakan cikin wata Sanarwa da aka rabawa manema labarai, yau Talata a Bauchi.
Kazalika shima a nasa bangaren Kwamishinar yan sandan jihar Umar Sanda ya tabbatar da janye dokar hana zirga-zirga.
Yace jami’an su zasu ci gaba da tabbatar da kowa yana bin doka yadda ya kamata, kuma tare da ganin ba a kara samun rikicin makamancin wannan ba.