Da ake yin duk wani sauyi a minti na karshe, za a bayyana Gwamna Simon Lalong na jihar Filato a matsayin babban darakta na kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na dan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.
Daily trust ta tattaro cewa Lalong, Kirista ne, an nada shi ne a matsayin babban darakta sakamakon hayaniyar da ta barke kan tikitin takarar Musulmi da Musulmi na APC.
Idan za a iya tunawa, manyan masu mukamai na jam’iyyar APC sun zabi Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna a matsayin babban darakta, yayin da aka zabi tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben.
Sai dai kuma an tattaro cewa bayan wata ganawa da Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima da na kungiyar gwamnoni (PGF) suka yi a Legas, an amince da a nada Lalong a matsayin shugaba domin a kwantar da hankulan al’ummar Kirista da kuma jin haushin Kiristocin Arewa.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Taron wanda aka fara a ranar Litinin da daddare ya kare a jiya.
Wata majiya mai tushe a taron ta ce, “Eh, Gwamna Lalong shine babban daraktan Jam’iyyar APC ta hada kai kuma mun kuduri aniyar ceto kasar nan daga masu son raba kan mu ta hanyar addini.”
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/wata-babbar-kotu-ta-raba-auren-shekara-23-da-aka-yi-tsakanin-wani-mutum-da-jikarsa/
El-Rufai, wanda ya bayyanawa manema labarai bayan taron, ya tabbatar da cewa an yanke shawara kan shugaban, yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan sauran mukamai a majalisar yakin neman zaben.
Ya ce, “An yanke shawara a kan babban daraktan, amma har yanzu ana tattaunawa kan wasu mukamai a kwamitin yakin neman zaben. Za a sanar da shugaban kasa da shugaban jam’iyya da kwamitin ayyuka na kasa (NWC) kafin a fitar da sanarwar a hukumance.”
Ya ci gaba da cewa gwamnonin sun je Legas ne domin su ba da rahoton aikin da Tinubu da abokin takararsa suka ba su na fara tuntubar juna da samar da tsarin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa.
Ya bayyana cewa, “Mun zo ne domin mu kawo rahoto kan wani aiki da dan takararmu na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da abokin takararsa suka ba mu domin fara tuntubar juna da samar da tsarin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa.
“Mun yi wasu ayyuka a kai. Mun yi wa dan takara da abokin takararsa bayanin kuma an dauki bayanai kuma fatanmu shi ne nan da dan kankanin lokaci dan takarar ya kara tuntubar shugabannin jam’iyyar ya kuma yi wa shugaban kasa bayani sannan ya samu nasa ra’ayin sannan mu kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a hukumance. .”
Sauran gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Abdullahi Ganduje na (Kano), Atiku Bagudu na (Kebbi), Abubakar Badaru na (Jigawa), Bello Matawalle ma (Zamfara) da Babajide Sanwo-Olu na (Lagos).
Sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata Iyiola Omisore, Adams Oshiomohole da Alhaji Kabiru Masari sun halarci taron.