Mataimakin shugaban kungiyar, Emeka Eziakonwa, shi ne ya bayyana hakan a yayin taron da aka shiryawa wadanda suke shirye-shiryen yin ritaya daga makarantar a garin Owerri a ranar Talata.
Kungiyar ‘Imo Community’ na Tampa Bay, dake zaune a Amurka, ta tallafawa Dalibai 10 dake karatu a Makarantar kimiyya da fasaha na gwamnatin tarayya dake Nekede da naira miliyan 1.
Da yake bayyana tallafin, Eziakonwa ya ce sun yi hakan ne domin tallafawa daliban dake zuwa makarantar domin sauya rayuwarsu ta fuskancin neman ilimi.
Ya ci gaba da cewa; kungiyar za ta ci gaba da ba da irin wannan tallafin daidai karfinta domin ganin suma sun shiga sahun masu ba da tallafi ta fuskancin ilimi da bunkasa bangaren ilimin dalibai dake karatu a makarantun kimiyya da kuma sauran al’umma baki daya.
Eziakonwa, ya ce tallafin za su rika yinsa a duk shekara, inda ya jinjinawa hukumar makarantar bisa bunkasa karatun makarantar.