Biyo bayan tafiyar Gareth Bale zuwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham a matsayin aro na tsawon shekara guda tuni aka duba cancanta aka baiwa Marcos Assensio lamba 11 ya sanya a bayansa domin fara sabuwar kakar wasa a leda.
‘Yan wasa da dama sun sanya lamba 11 a Real Madrid kamar su Michael Owen da Ronaldo de Lima da Karim Benzema da shi kamnsa Gareth Bale da sauran ‘yan wasa da dama kuma shima yanzu gashi an baiwa Marcos Assensio ita.
Ita kuwa lambar da Assensio yake sanyawa wato lamba 20 tuni aka baiwa Vinicious ita duba da cewar zaratan matasan ‘yan wasa ne a ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Real Madrid masu jini a jika kuma suna bayar da gudun mawa yadda ya kamata.
Assensio dai a kakar wasan data gabata ya baisami damar bayar da gudun mawa sosai ba a Real Madrid biyo bayan watanni daya kwashe yana fama da jinya sai dai daga ƙarshen kakar wasan Laliga yayi bajinta sosai wanda koda a ranar daya dawo daga rauni daya fara buga wasansa sai da ya jefa ƙwallo a raga kuma koda a wasan ƙarshe ba gasar ta Laliga shine ya jefa ƙwallo ta ƙarshe da Real Madrid ta jefa a gasar Laliga.