Hukumar kula da Ƴan sanda ta Kasa an bata sati biyu ta kammala binciken data ke yi akan tuhumar Mataimakin Kwamishinan Ƴan sanda na Ƙasa Abba Kyari da Hushpuppi.
Wannan na kunshe ne a cikin wata da Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Ikechukwu Ani ya sanyawa hannu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tallafin Karatu: Sanata Uba Sani ya yaba da yunkurin Gwamna Mai Mala Buni
Kwamishinan ya umarci ƴan sanda dasu tabbatar an gudanar da binciken yadda ya kamata.
Umarnin ya biyo bayan zaman taron Hukumar da tayi a Abuja, wanda ya samu jagorancin Tsohon Sufeto-Janar na Ƴansanda kuma Shugaban Hukumar Ƴansanda Musiliu Smith.
Idan dai za’a tuna, an dakatar da Kyari a ranar 1 ga watan Ogustan Shekarar 2021, biyo bayan shawarwari Sufeto-Janar na Ƴansanda Usman Baba ya bayar, akan zargin sa dasa hannu a wata almundahana akan rikakƙen dan Damfarar nan Ramon Abbas da akafi sani Hushpuppi