Biyo bayan komawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Athletico Madrid da shahararren thohon ɗan wasan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Ajax da Liverpool harma da Barcelona wato Luiz Suarez kuma ɗan asalin ƙasar Uruguay mai shekaru 33 ya sa mai horas wawa Diago Simeone ya bashi lamba 9.
Luis Suarez dai yaso ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus dake ƙasar Italiya amma kuma abin yaci tura shine daga baya aka ƙulla yarjejeniya tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Barcelona da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Athketico Madrid inda tuni ya kammala komawa can birnin Madrid.
Sai dai ko a jiya anji abokin Suarez na Barcelona wato Leonel Messi yana maganar cewar baiji daɗin irin rabuwar da akayi tsakanin Luis Suarez da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ba domin kuwa ba rabuwar daɗi sukayi ba ganin cewar lallai Barcelona korarsa sukayi tunda tun bayan zuwan sabon mai horas wa Roland Koeman ya bayyana cewar Suarez baya cikin tsarin tafiyarsa.
Sai dai masaan na hanin Barcelona kamar sun kashe maciji ne basu sare kan ba ganin cewar sun bar Luis Suarez yaci gaba da zama a ƙasar Andalus kuma a Athletico Madrid inda kuma duk shekara sai sun fafata a tsakaninsu kamar sau 2 ko sau 4.
Ana ganin cewar matuƙar zasu fafata a tsakaninsu zai iya yiwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona illa wajen zuramusu ƙwallaye ko dan irin wulaƙancin da sukayimasa a wajen rabuwarsu kamar yadda wasu ‘yan wasan suke yiwa wasu ƙungiyoyin idan sun tashi rabuwa kuma idan suka haɗu su ragargajesu yadda sukeso.
Suarez dai ya bayyana cewar zai baiwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Athletico Madrid gudun mawa a ƙarƙashin jagorancin mai horas wa Diago Simeone musamman a wannan sabuwar kakar wasan da aka fara wato kakar wasa ta 2010 zuwa 2021 kenan inda tuni aka fafata wasannin mako na biyu a gasar ta Laliga.
Luis Suarez dai ɗan wasa ne mai bayar da gudun mawa sosai idan yana fafata wasan ƙwallon ƙafa kuma shina ana yimasa kirari da idonsa idon raga domin baya wasa wajen jefa ƙwallo a zare idan dai har ya sami yadda yakeso wato tazomasa a dai dai, babban misali shine irin ƙwallayen dayake zazzagawa a zare ako yaushe.