• About Us
  • Blog
  • Gwamnatin Jihar Kano ta ce ana gabda fara ginin masana’antun Iskar Gas a Jihar
  • Home
Monday, March 20, 2023
  • Login
Dimokuradiyya
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
Dimokuradiyya
No Result
View All Result
Home Labarai

An Bankado Makarkashiyar Canza Dokokin Majalisar Wakilai Ta Kasa

Mustapha Haruna Dabai by Mustapha Haruna Dabai
May 15, 2019
in Labarai
Reading Time: 3 mins read
0 0
0
0
SHARES
3
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

An bankado wani shiri da wasu wakilan Majalisar wakilai ta kasa suke yi na ganin an canza wasu dokokin Majalisar kafin kaddamar da sabuwar majalisar ta 9 a farkon wata mai kamawa. An ce tuggun da ake kitsawan ya shafi na canza wasu dokoki ne da suka shafi sashen zaben Kakakin Majalisar da mataimakin sa, inda masu wannan hankoron suke neman a cire sashen da ke cewa, wanda zai ci zaben zama Kakakin majalisar ko mataimakinsa, tilas ne ya sami lashe rabin kuri’un majalisar da kuma doriyar kuri’a guda a sama. Kamar yanda abin yake a dokar majalisar a halin yanzun, in har da zababbun wakilan majalisar su 360 za su zauna a cikin majlalisar a lokacin gudanar da zaben, in dai har akwai ‘yan takaran neman zama Kakakin majalisar ko mataimaki sama da guda daya, to ya zama tilas ga duk wanda zai lashe zaben ya sami kuri’u 181 sannan ne zai iya zama Kakakin Majalisar. To amma a karkashin tuggun da masu son a soke wannan dokar suke shiryawa, suna so ne a kawar da wannan dokar, a maimakin hakan ya kasance duk wanda dai yake da kuri’u mafiya rinjaye ko yaya ne shi ne zai zama sabon Kakakin majalisar, ko da bai samu yawan kuri’u 181 ba. Hakanan a dokar majalisar ta Biyu sashe na 3 (g), tana cewa: in ya kasance akwai sama da zababbun ‘yan majalisar daya da suka tsaya a zaben, to sai a gudanar da zaben kamar yanda doka ta 3 (f) ta tanada, inda ta ce, duk wanda ya sami sama da rabin kuri’un da aka kada shi ne zai kasance zababben Kakakin majalisar. Sai dai, dokar kuma ta ce, in kuma har ya kasance cikin ‘yan takaran babu wanda ya sami rabin kuri’un da aka kada, to a nan sai a cire dan takaran da ya sami mafi karancin kuri’u, a kuma sake wani sabon zaben a tsakanin sauran ‘yan takaran da suke da mafiya yawan kuri’u, a tsakanin na gaba da wanda ke biye masa. A wannan tuggun ana nufin dai kawai a bar duk wanda ya sami kuri’u mafiya rinjaye ko dan yaya ne a matsayin shi aka zaba a matsayin Kakakin Majalisar. Wannan sabuwar dokar, in ji majiyoyin namu, sun yi daya ne da na zaben shugaban Majalisar Dattijai da mataimakin sa, inda duk dai wanda ke da kuri’u mafiya rinjaye shi ya ci zabe. Wakilinmu ya sami labarin cewa, duk wannan tuggun yana fitowa ne daga wakilan babbar Jam’iyyar adawa ta PDP, a kokarin da suke yi na ganin daya daga cikin su ne ya lashe zaben zama Kakakin Majalisar ba tare da wata tantama ba. majiyarmu ta tabbatar mana da cewa, wani sashe na wannan tuggun shi ne, su wakilan babbar jam’iyyar hamayyan za su tura wani daga cikin wakilan jam’iyyar ta APC domin ya tsaya takaran shugabancin majalisar, domin ya kalubalanci zabin da uwar jam’iyyar ta APC ta yi tun da farko, inda ta tsayar da Femi Gbajabiamila (APC Legas) wanda a yanzun haka shi ne shugaban masu rinjaye na majalisar, a matsayin dan takaranta na kujerar shugaban majalisar. To da zaran Femi Gbajabiamila, da kuma wani dan takaran shi ma daga jam’iyyar ta APC sun tsaya takaran a lokacin gudanar da zaben, sai kuma wakilan jam’iyyar ta PDP a majalisar su kuma su tsayar da wani daga cikin su takaran, da hakan ‘yan takaran sun zama su uku kenan, biyu daga jam’iyyar APC, daya kuma daga jam’iyyar PDP. Duk da sanin cewa, dan takara yana da damar janyewa a zabe kafin a fara kada kuri’a, to amma makarkashiyar ta tanadi cewa, duk wani dan takaran da masu kisisnar za su nemi da ya tsaya a zaben daga jam’iyyar ta APC, za su tabbatar da cewa, ba wanda zai daga wa Femi Gbajabiamila, kafa ne ba komai runtsi. Hakan zai baiwa wakilan jam’iyyar adawar ta PDP damar dunkule kuri’un su kaf su kadawa dan’uwansu a wajen zaben, sa’ilin da ita jam’iyyar APC ta raba nata kuri’un gida biyu kenan. Wanda hakan zai ba da dama ga dan takaran jam’iyyar adawan ya lashe zaben. Majiyar tamu ta ce, kwatankwacin hakan masu kisisnar suke son aiwatarwa a zaben mataimakin Kakakin majalisar. “Suna so ne su hada kai da shugabannin majalisar ta yanda za su yi mana bazata su canza dokokin majalisar, kamar yanda wasu suke zargin an yi hakan a wajen zaben Shugaban majalisar Dattijai a shekarar 2015. “Bazata suke son su yi mana, amma tuni mun hango su, mun kuma sami labarin wannan tuggun na su. “A gaskiya, sun su so boye shirin na su ne, face kadan ne daga cikin su za su san abin da ake ciki, sai dai kawai a ranar zaben su fito da shirin na su but, su ba mu mamaki. Ta yanda komai zai gudana tamkar a was an kwakwayo. A dai wannan sabuwar Majalisar ta 9, Jam’iyyar APC tana da wakilai 224 ne, Jam’iyyar PDP ita kuma tana da wakilai 122, sa’ilin da sauran jam’iyyun adawa suke da wakilai 14.

Previous Post

Kotu Ta Tarwatsa Sabbin Sarakunan Da Ganduje Ya Nada

Next Post

Gwamnan Bauchi Da Kwamishinan ‘Yan Sanda Sun Sha Alwashin Magance Matsalar Tsaro

Next Post

Gwamnan Bauchi Da Kwamishinan ‘Yan Sanda Sun Sha Alwashin Magance Matsalar Tsaro

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result
Arabic Arabic English English French French Hausa Hausa
  • Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    2455 shares
    Share 982 Tweet 614
  • Da Ɗumi-Ɗuminsa: Ƙazamin Rikici Ya Kaure Tsakanin Shugaban Ƙungiyar CAN Da Isa Ashiru Kudan

    1995 shares
    Share 798 Tweet 499
  • Sai na yi lalata da kai na kwanaki 4 babu ƙaƙƙautawa sannan zan taimaka maka, Wata mata ga saurayi

    1693 shares
    Share 677 Tweet 423
  • Ga Irinta Nan: Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Ƙi Amsar Cikin Da Ya Ɗirka Mata

    1365 shares
    Share 546 Tweet 341
  • CBN Ya Sake Fitar Da Sabbin Bayani Kan Dawo Da Tsofaffin Takardun Kudin Naira

    1592 shares
    Share 637 Tweet 398
Yanzu-Yanzu: Zanga-zangar Karancin Kudin Naira Tana Cigaba Da Yaduwa

DA DUMI-DUMINSA: Jam’iyyar APC Ta Lashe Zaben Gwamnan Jihar Ebonyi

March 20, 2023
Gwamna Umahi Ya Kori Wasu Mataimakansa Sa’o’i 48 Bayan Kammala Zabe

Gwamna Umahi Ya Kori Wasu Mataimakansa Sa’o’i 48 Bayan Kammala Zabe

March 20, 2023
INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato

INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato

March 20, 2023
PDP Ta Lashe Kujeru 28 Na Majalisar Dokoki, Yayin Da APC Ta Tsira Da Hudu

PDP Ta Lashe Kujeru 28 Na Majalisar Dokoki, Yayin Da APC Ta Tsira Da Hudu

March 20, 2023
Bayan Faduwa A Zaben Sake Darewa Kujerar Sanata Nnamani Ya Bar PDP

Bayan Faduwa A Zaben Sake Darewa Kujerar Sanata Nnamani Ya Bar PDP

March 20, 2023
Mohammed Ya Sake Lashe Zaben Gwamna Karo Na Biyu A jihar Bauchi

Mohammed Ya Sake Lashe Zaben Gwamna Karo Na Biyu A jihar Bauchi

March 20, 2023
Yanzu-Yanzu: Zanga-zangar Karancin Kudin Naira Tana Cigaba Da Yaduwa
Labarai

DA DUMI-DUMINSA: Jam’iyyar APC Ta Lashe Zaben Gwamnan Jihar Ebonyi

March 20, 2023
Gwamna Umahi Ya Kori Wasu Mataimakansa Sa’o’i 48 Bayan Kammala Zabe
Labarai

Gwamna Umahi Ya Kori Wasu Mataimakansa Sa’o’i 48 Bayan Kammala Zabe

March 20, 2023
INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato
Labarai

INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato

March 20, 2023
Yanzu-Yanzu: Zanga-zangar Karancin Kudin Naira Tana Cigaba Da Yaduwa

DA DUMI-DUMINSA: Jam’iyyar APC Ta Lashe Zaben Gwamnan Jihar Ebonyi

March 20, 2023
Gwamna Umahi Ya Kori Wasu Mataimakansa Sa’o’i 48 Bayan Kammala Zabe

Gwamna Umahi Ya Kori Wasu Mataimakansa Sa’o’i 48 Bayan Kammala Zabe

March 20, 2023
INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato

INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato

March 20, 2023

Twitter

Archives

Recent Posts

  • DA DUMI-DUMINSA: Jam’iyyar APC Ta Lashe Zaben Gwamnan Jihar Ebonyi
  • Gwamna Umahi Ya Kori Wasu Mataimakansa Sa’o’i 48 Bayan Kammala Zabe
  • INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato

Quick Links

  • Tsaro
  • Siyasa
  • Labarai
  • Wasanni
  • Kasuwanci
  • Rikicin Duniya

Contact Us

info@dimokuradiyya.com.ng

0809 912 4425 +234 809 912 4425

No. 218 Mogadishu layout Kaduna City Center Ahmadu Bello way kaduna. Kaduna, Nigeria 800273

Copyright © 2022 Dimokuradiyya Media Services LTD.

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio

Copyright © 2022 Dimokuradiyya Media Services LTD.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In