• About Us
  • Blog
  • Gwamnatin Jihar Kano ta ce ana gabda fara ginin masana’antun Iskar Gas a Jihar
  • Home
Saturday, June 3, 2023
  • Login
Dimokuradiyya
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
Dimokuradiyya
No Result
View All Result
Home Labarai

An Bankado Sunan Wacce Ta Dauki Bidiyon A’isha Buhari Tana Masifa

Mustapha Haruna Dabai by Mustapha Haruna Dabai
October 14, 2019
in Labarai, Siyasa
Reading Time: 4 mins read
0 0
0
1
SHARES
5
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Baraka ta kunno kai a Fadar Shugaban Najeriya a daidai lokacin da ake yada jita-jitar cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai yi wa matarsa kishiya.

A ‘yan kwanakin nan wani bidiyo ya rika yawo a shafukan sada zumunta wandaa cikinsa aka ga uwargidan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tana ta fada da harshen turanci tana gaurayawa da Hausa.

Jama’a da dama a shafukan sada zumunta sun rinka alakanta wannan bidiyon da cewa Aisha Buhari ce ta dawo daga Ingila tana fada cewa an rufe mata kofa.

BBC ta samu jin ta bakin Aisha Buhari inda ta tabbatar da cewa ita ce aka dauka a cikin bidiyon amma ta ce tsohon bidiyo ne.

Ta kuma yi karin haske cewa Fatima ‘yar gidan Mamman Daura ce ta nadi bidiyon da ake tafka mahawara a kai.

Sai dai ko da BBC ta tuntubi Fatima Mamman Daura, ba ta musanta daukar bidiyon ba, sai dai ta ce ta dauki bidiyon ne domin ta nuna wa iyayenta da jami’an tsaro a matsayin shaida ko da wani abu ka biyo baya.

Me Aisha Buhari ta ce?

Bayan saukar Aisha Buhari a filin jirgi a Abuja, ta samu ganawa da ‘yan jarida inda ta yi bayanai da harshen Hausa da kuma turanci.

A cikin bayanin da ta yi a harshen turanci, ta bayyana cewa lallai ita ce a wannan bidiyo kuma lamarin ya faru ne a cikin fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ta ce: “Jami’an tsaro na suna wurin amma sun kasa yin komai domin ‘yar gidan Mamman-Daura Fatima ce ta dauki bidiyon kuma har yau ni da su mun kasa yin komai kan lamarin.”

Haka zalika a hirar da aka yi a harshen Hausa ta nanata cewa Fatima ce ta dauki bidiyon, har tana yi ma ta dariya kuma ita ce ta rufe ma ta kofar dakin ajiyar kayayyaki.

Me Fatima Mamman Daura ta ce?

A hirarta da BBC, Fatima ta bayyana cewa tun bayan hawan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, shugaban ya bai wa mahaifinta (Mamman Daura) wurin zama a cikin fadar shugaban kasa wanda ake kira ”Glass House.”

Ta ce a lokacin da Yusuf Buhari ya samu hatsari a kwanakin baya, Shugaba Buhari ya bukaci Mamman-Daura da ya koma wani gida da ake kira ”House No. 8”, wato gida mai lamba 8 domin a yi jinyar Yusuf a gidan da Mamman Daura da iyalensa suke zaune domin wurin ya fi kusa da inda Aisha Buhari ta ke.

Fatima ta bayyana cewa ko da hakan ya faru iyayenta ba su Najeriya, sai dai mahaifinta ya ba ta umarnin ita da ýar uwarta, cewa su kwashe kayansu daga gidan a ranar wata Asabar.

Ta bayyana cewa suna cikin kwashe kayansu ne sai ta ji hayaniya, domin ita tana can cikin kuryar daki ‘yar uwarta kuma tana dakin waje wanda ya fi kusa da kofar shiga gidan.

Ta ce kofar da ke waje an saka mukulli an rufe domin yawanci idan suna ciki su kan rufe ta.

Ta bayyana cewa ko da Aisha ta zo ta ga kofar a rufe, ”ta yi amfani da kujerar karfe wajen balle kofar.”

A cewar Fatima, wannan dalili ne ya sa ta dauko waya domin yin bidiyo don ya zama shaida.

Shin akwai ‘yar tsama tsakanin iyalin Mamman Daura da Aisha Buhari ne?

An dade ana jita-jita musamman a kafofin sada zumunta cewa Aisha Buhari ba ta ga maciji da Mamman-Daura wanda yake amini ne ga shugaban kasa kuma dan uwansa ne na jini.

Ko a wurin taro ta sha yin shagube kan wasu mutane da ake zargin sun zagaye shugaban kasa sun hana shi aiki duk da cewa ba ta taba ambatar sunansa ba.

Amma da alama a wannan karon tura ta kai bango tun da har ta kama suna kuma ta ce an kasa yin wani abu sakamakon ‘yar gidan Mamman Daura ce.

Ko da BBC ta tambayi Fatima Mamman-Daura ko tun can dama ana samun rashin jituwa tsakanin Mamman-Daura da Aisha Buhari, ta bayyana cewa kafin Shugaba Buhari ya hau kan karagar mulki, suna zumunci lafiya kalau, amma tun bayan nan ne komai ya sauya aka fara samun matsaloli.

Previous Post

An Tashi Kunnen Doki Tsakanin Nijeriya Da Brazil

Next Post

Hafsat (Barauniya) Ta Lashe Kyautar Jarumar Kannywood

Next Post

Hafsat (Barauniya) Ta Lashe Kyautar Jarumar Kannywood

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result
  • Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    2600 shares
    Share 1040 Tweet 650
  • Batun Dakatar Da Opay Da Palmpay, CBN Ya Bayyana Gaskiyar Zance

    2342 shares
    Share 937 Tweet 586
  • Da Ɗumi-Ɗuminsa: Ƙazamin Rikici Ya Kaure Tsakanin Shugaban Ƙungiyar CAN Da Isa Ashiru Kudan

    2129 shares
    Share 852 Tweet 532
  • Sai na yi lalata da kai na kwanaki 4 babu ƙaƙƙautawa sannan zan taimaka maka, Wata mata ga saurayi

    1904 shares
    Share 762 Tweet 476
  • Ga Irinta Nan: Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Ƙi Amsar Cikin Da Ya Ɗirka Mata

    1439 shares
    Share 576 Tweet 360
Wasu Maƙota Sunyi Musayar Matansu Sakamakon Kama Junansu Da Kwartanci

Wasu Maƙota Sunyi Musayar Matansu Sakamakon Kama Junansu Da Kwartanci

June 3, 2023
Yadda Farashin Man Fetur Ya Hauhawa Cikin Kankanin Lokaci Bayan Sanarwar Cire Tallafin

Shugaba Tinubu Ya Jajantawa kasar Indiya kan Hadarin Jirgin Kasa

June 3, 2023
Cire Tallafi Man Fetur: NUJ Ta Umarci Mambobin Ta Da Su Marawa NLC Baya

Cire Tallafi Man Fetur: NUJ Ta Umarci Mambobin Ta Da Su Marawa NLC Baya

June 3, 2023
Dan Wasan Gaba Na Real Madrid Ya Daura Damarar Barin Kungiyar

Dan Wasan Gaba Na Real Madrid Ya Daura Damarar Barin Kungiyar

June 3, 2023
Ta Kashe Sama Da Naira 100,000 A Labulen Ɗakin Da Ta Kama Haya

Ta Kashe Sama Da Naira 100,000 A Labulen Ɗakin Da Ta Kama Haya

June 3, 2023
Bani da Wani Shirin Komawa APC — Gwamnan G5

Bani da Wani Shirin Komawa APC — Gwamnan G5

June 3, 2023
Wasu Maƙota Sunyi Musayar Matansu Sakamakon Kama Junansu Da Kwartanci
Al'ajabi

Wasu Maƙota Sunyi Musayar Matansu Sakamakon Kama Junansu Da Kwartanci

June 3, 2023
Yadda Farashin Man Fetur Ya Hauhawa Cikin Kankanin Lokaci Bayan Sanarwar Cire Tallafin
Labarai

Shugaba Tinubu Ya Jajantawa kasar Indiya kan Hadarin Jirgin Kasa

June 3, 2023
Cire Tallafi Man Fetur: NUJ Ta Umarci Mambobin Ta Da Su Marawa NLC Baya
Labarai

Cire Tallafi Man Fetur: NUJ Ta Umarci Mambobin Ta Da Su Marawa NLC Baya

June 3, 2023
Wasu Maƙota Sunyi Musayar Matansu Sakamakon Kama Junansu Da Kwartanci

Wasu Maƙota Sunyi Musayar Matansu Sakamakon Kama Junansu Da Kwartanci

June 3, 2023
Yadda Farashin Man Fetur Ya Hauhawa Cikin Kankanin Lokaci Bayan Sanarwar Cire Tallafin

Shugaba Tinubu Ya Jajantawa kasar Indiya kan Hadarin Jirgin Kasa

June 3, 2023
Cire Tallafi Man Fetur: NUJ Ta Umarci Mambobin Ta Da Su Marawa NLC Baya

Cire Tallafi Man Fetur: NUJ Ta Umarci Mambobin Ta Da Su Marawa NLC Baya

June 3, 2023

Twitter

Archives

Recent Posts

  • Wasu Maƙota Sunyi Musayar Matansu Sakamakon Kama Junansu Da Kwartanci
  • Shugaba Tinubu Ya Jajantawa kasar Indiya kan Hadarin Jirgin Kasa
  • Cire Tallafi Man Fetur: NUJ Ta Umarci Mambobin Ta Da Su Marawa NLC Baya

Quick Links

  • Tsaro
  • Siyasa
  • Labarai
  • Wasanni
  • Kasuwanci
  • Rikicin Duniya

Contact Us

info@dimokuradiyya.com.ng

0809 912 4425 +234 809 912 4425

No. 218 Mogadishu layout Kaduna City Center Ahmadu Bello way kaduna. Kaduna, Nigeria 800273

Copyright © 2023 Dimokuradiyya Media Services LTD.

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio

Copyright © 2023 Dimokuradiyya Media Services LTD.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In