Matan Sojojin da jami’an Soji sun yi kira da’a biyasu diyyar rayuwa domin ɗaukar nauyin kula da yaran su.
Matan sun yi ƙawanya ne domin bikin tunawa da ƴan mazan jiya a Minna, Jahar Niger a ranar Asabar, inda suka ce an banzantar dasu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Seria A: An kori Shevchenko a Matsayin Kocin Genoa
Rahmatu Abdul Abugi ɗaya daga cikin zawarawan tace mijinta Captain A.A. Abugi an kashe shi yana aiki a Maiduguri Jahar Borno a ranar 5 ga watan Ogusta na shekarar 2014, kuma tun daga lokacin, duk ƙoƙarin su na ganin an biyasu diyyar ranshi basu samu dama ba.
“Muna son Gwamnati da Rundunar soji data taimaka mana. Mijina ya mutu akan hanyar gudanar da aiki, gwamnati da Rundunar soji tana buƙatar ta taimaka mana.
Acewar Nabila Abdullahi Usman, da Sakataren Matan da mazajen su, suka mutu ta Jahar Niger Mohammed Goje an kashe shi a Damaturu Jahar Yobe shekaru biyar.
Tayi kira ga mahukunta a soji dasu taimaka wajen ɗaukar nauyin karatun ƴaƴen su