Babban bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa naira miliyan ɗaya (N1m) na sababbin kuɗi yake ba rassan bankuna kullum a jihar Legas.
Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa kuɗin sun yiwa mutane kaɗan a jihar, inda dubunnan mutane ke kwashe lokaci mai tsawo wajen bin layin cirar kuɗin a ATM.
KU KARANTA KUMA: CBN ya yaudari Buhari akan sake fasalin kuɗin naira -Oshiomole
Masu sharhi sun yi amanna cewa ko dai babban bankin baya da isassun sababbin kuɗin ne ko kuma da gangan yake hana bankuna su saboda wani ɓoyayyen dalili wanda ba a sani ba.
Haka kuma, bankunan kasuwanci sun ƙi su bayyana adadin sababbin kuɗin da CBN yake basu a kowane mako.
Wani ma’aikacin bankin Sterling Bank, wanda ya nemi da a sakaya sunan sa, yace naira miliyan ɗaya (N1m) bankin yake karɓa domin rabawa kowane reshensa a mako a jihar Legas.
“Wannan dalilin ne ya sanya rassan mu suke bayar da sababbin kuɗin a kullum. Bamu da rassa sosai kamar sauran bankunan, amma muna bayar da kuɗi a ATM da kan kanta.” Majiyar ta shaidawa Legit.ng
Wasu daga cikin bankuna na fargabar bayyana adadin sababbin kuɗin da CBN yake ware musu kowane mako, saboda tsoron fuskantar hukunci.
Haka kuma, CBN ya ƙi ya wallafa adadin sababbin kuɗin da yake turawa bankuna a kowane mako.
Abdulkadir Jubrin, wane ma’aikacin CBN a jihar Bauchi, yace bankin a kullum yana bayar da naira miliyan talatin (N30m) na sababbin kuɗi ga kowane reshe.
Sai dai wannan iƙirarin na Jibrin, bankin CBN bai tabbatar da shi ba kuma bai musanta shi ba.
Shugaba Buhari yayi baƙin ciki matuƙa da wahalar da ƴan Najeriya ke sha kan sababbin kuɗi -Minista
A wani labarin na daban kuma, shugaba Buhari ya damu matuƙa da halin da ƴan Najeriya suka shiga saboda sababbin kuɗaɗen naira.
Ministan kuɗi, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa shugaba baya jindaɗin wahalar da ƴan Najeriya ke fuskanta saboda sababbin kuɗaɗen naira.
Zainab Ahmed ta bayyana hakan ne yayin da take magana a wajen wani taron ministoci a faɗar shugaban ƙasa.