Hukumar Alhazai ta babban birnin Tarayya ta amince da a biya Naira milyan 1.5 a matsayin kudin aikin hajji na shekarar 2019, ga maniyyatan da suke son tashi daga Abuja din. Jami’in yada labarai na hukumar, Muhammad Lawal, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya kuma ce, duk maniyyatan da za su tashin daga Abuja, an kayyade masu samun kudin canjin kudaden waje Dala 800, kamar yanda hukumar aikin hajjin ta ta kasa NAHCON, ta kayyade. Ya bayyana cewa, karin da aka samu din a kan kudin aikin hajjin a bisa yanda alhazan suka biya a shekarar 2018 da ta gabata, ya faru ne a sakamakon karin da aka samu a kan ayyukan da ake yi wa alhazawan a can kasa mai tsarkin, da kuma karin da aka samu a kan canjin Naira zuwa dala. Kakakin ya nanata tabbacin da hukumar ta bayar na yin duk abin da take iyawa na ganin ta yi wa alhazan na wannan shekarar ta 2019, duk abin da ya kamata. Ya bayyana cewa, duk ma’aikatan hukumar sun sami horo sosai kan yanda za su kyautata aikin na su. Ya kuma bayyana kiran da hukumar ke yi ga dukkanin alhazan da suka fara ajiya a asusun aikin hajjin da su hanzarta cika sauran kudin kafin nan da ranar 31 ga watan Mayu, domin hukumar ta sami cimma wa’adin da uwar hukumar ta kasa ta ba ta. Lawal, ya gargadi masu nufin zuwa aikin hajjin wadanda kuma kawo yanzun ba su mayar da fom din da aka ba su su cike ba da su hanzarta yin hakan kafin wa’adin ya kare, ko kuma su zargi kansu in sun kasa yin hakan. Ya kuma shawarci mazauna babban birnin tarayyan da suke da nufin zuwa aikin hajjin ta hannun hukumar alhazan da su yi rajista da jami’an hukumar da ke sassan babban birnin tarayyan shida da ke Sakatariyoyin birnin shida kafin karshen wannan watan.