Hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar turai wato Uefa ta bayyana ranar da zata rabba rukunin gasar zakarun nahiyar turai da ake kira da Uefa Champions League a turance wato sabuwar kakar wasa kenan mai kamawa ta 2020 zuwa 2021.
Inda hukumar ta bayyana ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar da ake ciki ta 2020 domin raba rukunin ga dukkanin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan da suka sami tikitin buga sabuwar kakar wasan da za’a shiga.
Za’a raba wannan rukuni a birnin Nyon dake ƙasar Switzerland a can yankin nahiyar ta turai kenan a waccan rana ta 1 ga watan mai kamawa kenan inda ko wacce ƙungiya zatasan abokan karawarta na rukuni.
A kakar wasan da ta gabata dai ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich dake ƙasar Jamus ita ce ta zamo zakara bayan da tasha da kyar a hannun ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris Saint Germain daci 1 da nema ta hannun ɗan wasan ƙasar Faransa wato Coman.
Sannan Munich ta kafa babban tarihin da zaiyi wuya a sami wata ƙungiyar ƙwallon ƙafan da zata gogeshi wato na lashe dukkanin wasannin ta tun daga rukuni har zuwa wasan ƙashe inda koda kunnen doki batayi ba, sannan kuma ta lashe gasar karo na shida a tarhin inda ta buga wasannin ƙarshe guda 11 ta lashe 6 ta ɓarar da guda 5.