Jam’ian Yan sanda sun yi nasara halaka wasu masu garkuwa da muatne guda biyu a Anguwar Hausawa dake yankin Naharati a karamar Hukumar Abaji dake birnin tarayya Abuja.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kashe masu garkuwan ne yayin wata musayar wuta da Ƴan Sanda da kuma Jami’an Sintiri na Bijilanti dake Kula da yankin.
Wani Mazaunin yankin da aka bayyana shi da Suleiman ya shaida cewa Masu garkuwa da mutanen sun kutsa Unguwar ce da talatainin dare inda suka rika kutsawa gidajen mutane a Anguwar ta Hausawa.
Ya ce Masu garkuwa da Mutanen Sun Fara cin karen su babu babbaka ta inda suka samu Nasarar ɗebe mutane huɗu gabannin zuwan Jam’ian tsaro.
Mutanen da aka yi Garkuwa da su din kamar yadda aka bayyana sun hada da wani mai suna Abdullahi Umar, Abdulkareem Yusuf, Abubakar Umar da kuma wani yaro ɗan Kimanin shekara 13 mai suna Abdulrahman Isah.
Tuni Shugaban Karamar Hukumar ta Abaji Alhaji Abdulrahman Ajiya ya tabbatar da labarin sace mutanen da kuma halaka masu garkuwan biyu.
Wakilin Jaridar Daily Trust ɗin ya garzaya ofishin yan sanda dake yankin inda ya tabbatar da gane wa idanun shi gawarwakin masu garkuwan da aka kashe, inda su ma al’ummar yanki suka garzaya don kashe Ƙwarƙwatar idanu.