Wadan su da ake zargin Yan bindiga ne sun kai samame Jihar Jigawa don har sun harbe mutun daya har lahira tare da raunata mutane Tara a take yanzu haka suna Asibiti.
Hakan ya faru a wani karamin gari mai suna Garin Maidawa dake gundumar Abiya cikin karamar hukumar Dutse, babban birnin jihar Jigawa.
Rahotanni sun tabbatar da cewar an aike da wadanda suka ji rauni Asibitin Rashid Shakoni dake gab da Garin Dan-masara dake Birnin Dutse.
Lokacin da yake karin bayani game da aukuwar Bala’in Kansilan gundumar,Abiya , Malam Safiyanu Abdu, yace Bala’in ya faru ne a daren Jiya Laraba.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da manema Labaru Kwamishinan Yan sanda a Jihar Jigawa, Bala Zama ya tabbatar da aukuwar labarin sai dai yace suna zargin Yan fashi da makami ne, kuma suna tsaka da gudanar da bincike.