A yau Asabar 18 ga watan Afrilun 2020, Ministan Sadarwa, Shaikh Isa Ali Fantami ya jagoranci Jana’izar Abba Kyari, inda bayan nan aka bizne gawar Malam Abba Kyari a makabartar Gudu da ke Abuja, Birnin Tarayyar Nijeriya.
Da ma gwamnatin Nijeriya ta ce ba za a yi taro ba a wurin jana’izar tasa.
Sai dai kuma mutanen da suka halarci bizne shi suna da dan yawa sannan kuma babu maganar bayar da tazara.