By Abbas Yakubu Yaura
Mataimakin shugaban hadin kan kungiyoyi kiyaye afkuwar hadura masu zaman kansu Yusuf Zubairu ya bukaci gwamnatin tarayya data aiwatar da shekaru goma na Majalisar Dinkin Duniya don kiyaye hadurra na shekarar 2021-2030.
Yace hakan zai taimaka wajen samar da hanyoyin da basu da hadari da kuma asarar rayuka.
Ya yi wannan jawabi ne a karshen makon daya gabata a Abuja, lokacin da kungiyar mata masu kula da hanyoyin kiyaye hadurra (ROSOWA) ta ziyarci asibitin Garki domin bayar da gudummawar kayayyaki ga wadanda abin ya shafa a kan tituna a wani bangare na gudanar da bukukuwan ranara tunawa da wadanda abin ya shafa akan tituna ta duniya.
Zubairu ya bayyana cewa rashin gudun wuce sa’a yana matakin farko wajen maganin rage afkuwar hadarurruka.
Sannan ya dorawa gwamnati alhakin bayar da shawarwari tare da hukunta masu laifi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Daraktan ayyuka na asibitin Garki, Dakta Kenneth Ityo, yace asibitin na kula da wadanda abin ya shafa da zarar an kai su asibitin.