Yan sanda a kasar Malawi sun cika hannu da wasu mutane biyu a kasar cikin har da babban mai tallafa wa shugaban kasar Lazarus Chakwera sakamakon runtumo wani kudiri izuwa kwaryar majalisa ba tare da sanin mahukunta ba.
Kudirin ya shigar gaban majalisar da zummar neman gwamnati ta sanya hannu kan ɗiba kuɗaɗen gwamnati ba tare da bin hanyoyi da suka wajaba ba.
Jaridar The Nation a Kasar ta ruwaito cewa babban mai tallafawa Shugaban Kasar ya shigar da kudirin ne ta hannun majalisar jihar inda ake neman gwamnati ta ware zunzurutun kudi har kimanin Euro miliyan 100 don gina gidaje wa jami’an yan sanda da na soji gami da ma’aikatan hukumar shige da fice ta kasar.
Sai dai Jaridar ta ce ya shiga da kudirin ne gaba gaɗi ba tare da sanin kowa ba.
Kuma tuni aka yi amannar cewa Pastor Thom Martin wanda shine mai tallafawa Shugaban Kasar, ke da alhakin wannan lamari.
Jima kaɗan bayan cafke shi ne kuma ofishin shugaba Chakwera ya fitar da takardar tsige.
Kawo yanzu dai babu wani martani daga Pastor Thom, to sai dai yan sanda sun ce za a gabatar da su ne a gaban kuliya nan ba da jimawa ba bisa zargin laifin hawan ƙawara wa ofis.