Jami’an Yan sanda dake Jahar Ogun sun cafke wani da ake zargi da laifin yin garkuwa da Soja, sannan ya cigaba da sanya kakin sojan yana aikata miyakun ayyuka da su.
Lamarin ya auku ne a Odo Pako Ota a karamar hukumar Ado Odo Ota dake Jahar Ogun. Kamar yadda Jaridar Channel Tv ta wallafa a shafinta
Shidai Wanda ake zargin yayi yunkurin kwace bindiga daga hannun Jami’in Yan sakai.
KARANTA:- TIRKASHI: An yankewa yahoo boy hukunci wankin bayi na kwana sittin
Jami’i mai magana da yawun Yan sanda na Jahar Abimbola Oyeyemi, cewa yayi Wanda ake zargin shine Waliu Olayede, yace an kama shine bayan rahoto da suka samu daga Yan sandan Sango Ota, CSP Godwin Idehai, inda yake cewa Yan Sakai suna samun sabani da wani Soja a yankin Odo Pako Kauyen Ota.
Dajin haka DSP ya bazama da mutanen sa zuwa inda wannan mutumin yake, suna zuwa suka ganshi cikin kakin soja baki daya, sai suka fara tambayarsa amma bai iya amsa tambayoyin ba, basuyi wata-wata ba, sai suka kwamusoshi zuwa Ofishin su. Don cigaba da bincike.
Bayan sun kawoshi ofishin, suka fara masa tambayoyi a ina ya sami wadannan kakin amma bai iya amsawa ba.
Nan take yan sandan suka cigaba da tsare shi.
Bayan Dan lokaci kadan sai suka samu rahoton cewa wannan da suka tsare shida wasu sunyi garkuwa da Jami’in soja ne, a ranar sha shida ga watan July, na wannan shekarar, da misalin karfe sha daya da rabi, inda suka tafi dashi wurin boyo a Alagbado Jahar Legas, suka kwace masa kakinsa da katin shaidarsa na soja, da katin cire kudi har guda uku da kuma wayarshi.
Oyeyemi yace sun cigaba da sanya kakin suna aikata wasu ayyukan laifi kamin a kama su.
Kwamishinan Ƴansandan Jahar ya bada umarnin tafiya dashi zuwa babban Ofishin su dake Jahar don cigaba da bincike a kanshi.
CP yasha alwashin cigaba da bincike kan duk masu laifi an kamasu sannan sun fuskanci hukunci.