Alkalin Alkalai kuma kwamishiniyar shari’a ta jihar Kaduna,Aisha Dikko ta ce an kama Janar din Sojan ne bisa karya doka na kin zaman gida.
Ta kara da cewa sojan yana sanye da kakinsa tare da wasu fasinja har mutum uku wanda dukkaninsu babu wanda yake sanye da takumkumin fuska.
Kamar yadda ta bayyanawa manema labarai, ta ce ” sojan ya bayyana kotun-tafi-da-gidan cewa yana kan hanyarsa ne daga Abuja domin gudanar da wani aiki”.
Har wa yau, kotun ta ci tarar ragowar mutane ukun bisa karya dokar kin zama a gida da kuma kin saka takumkumin fuska.
Kwamishiniyar ta kara da cewa fitaccen Malamin addinin nan wato Yusuf Rigachukun tare da dansa an kama su bisa karya dokar kulle. Sai dai Rigacukun ya bayyanawa kotun cewa an gayyace sa gidan rediyo ne domin yin wani shiri.
Amma duk da haka kotun ta ci tararsu Naira 5000 kowanensu saboda rashin takumkumin fuska.
Sai dai kotun ta umarci Malamin ya yi amfani da ikonsa wajen yin kira ga al’umma da su bi duk matakan da suka dace wajen kaucewa kamuwa da wannan cuta ta COVID19.
Daga: Abubakar Muhammad Usman